Abubakar Mahmoud Gumi — 1

1:1 Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

1:2 Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;

1:3 Mai rahama, Mai jin ƙai;

1:4 Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.

1:5 Kai muke bautawa, kuma Kai kadai muke neman taimakonKa

1:6 Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.

1:7 Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.[1]