Abubakar Mahmoud Gumi — 518

50:1 K. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma.

50:2 Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki."

50:3 "Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa."

50:4 Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurin Mu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.

50:5 Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa.

50:6 Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?

50:7 Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?

50:8 Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?

50:9 Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.

50:10 Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.

50:11 Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.

50:12 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, [1]da Samũdãwa.

50:13 Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.

50:14 Da ma'abũta ƙunci [1]da mutãnen Tubba'u,[2] kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.

50:15 Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.