Abubakar Mahmoud Gumi — 530

54:28 Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.

54:29 Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,

54:30 To, yãya azãbaTa take da gargaɗi Na?

54:31 Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.

54:32 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

54:33 Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.

54:34 Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.

54:35 Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.

54:36 Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙar Mu, sai suka yi musu game da gargaɗin.

54:37 Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩ Na."

54:38 Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.

54:39 To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩ Na.

54:40 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

54:41 Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.

54:42 Sun ƙaryata game da ãyõyin Mu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.

54:43 Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?

54:44 Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"

54:45 Zã a karya[1] tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.

54:46 Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.

54:47 Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.

54:48 Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."

54:49 Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.