Abubakar Mahmoud Gumi — 594

89:23 Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!

89:24 Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"

89:25 To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.

89:26 Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurin Sa.

89:27 Yã kai rai mai natsuwa!

89:28 Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).

89:29 Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyi Na (mãsu bin umurui a dũniya).

89:30 Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).

90:1 Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari[1] ba.

90:2 Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.

90:3 Da mahaifi da abin da ya haifa.

90:4 Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.

90:5 Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?

90:6 Yana cẽwa "Na[1] halakarda dũkiya mai yawa,"

90:7 Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?

90:8 Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?

90:9 Da harshe, da leɓɓa biyu.

90:10 Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi[1] biyu ba?

90:11 To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?

90:12 Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?

90:13 Ita ce fansar wuyan bãwa.

90:14 Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.

90:15 Ga marãya ma'abũcin zumunta.

90:16 Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.

90:17 Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.

90:18 Waɗannan ne ma'abũta albarka[1]