Abubakar Mahmoud Gumi — 602

106:1 Sabõda sãbon kuraishawa.

106:2 Sãbon su na tafiyar hunturu da ta bazara.

106:3 Sabõda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (Ka'abah).

106:4 wanda Ya ciyar da su (Ya hana su) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsõro.

107:1 Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?

107:2 To, wan nan shi ne ke tunkure marãya (daga haƙƙinsa).

107:3 Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.

107:4 To, bone yã tabbata ga masallata.

107:5 Waɗan da suke masu shagala daga sallar su.

107:6 Waɗan da suke yin riya (ga ayyukansu)

107:7 Kuma suna hana taimako.

108:1 Lalle ne Mu, Mun yi maka kyauta mai yawa.

108:2 Saboda haka, ka yi salla dõmin Ubangijinka, kuma ka sõke (baiko, wato sukar raƙumi).

108:3 Lalle mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka.